Fatma Samoura za ta kai ziyara Saliyo

Sakatariyar Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya,
Fifa, Fatma Samoura, za ta ziyarci Saliyo domin
sasanta rikici tsakanin hukumar kwallon kafar
kasar da shuwagabannin siyasar kasar.
Fifa ta bukaci yin taro tsakaninta da Shugaban
kasar Saliyo, Ernest Bai Koroma, da kuma
jami'an hukumar kwallon kafar kasar.
Haka kuma Samoura na son tattaunawa kan
batun cogen wasa da ya shafi Saliyo a shekarar
2008.
A shekarar 2014 aka dakatar da 'yan wasa 15 da
wasu jami'an Saliyo kan zargin cogen wasan da
suka yi da Afirka ta Kudu a wasan shiga gasar
cin kofin duniya.
Tun a farkon ba ne hukumar kwallon kafa ta
Saliyo ta kafa kwamitin bincike ta kuma mikawa
shuwagabannin kasar abin da ta gano, amma har
yanzu ba a dauki mataki ba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Fatma Samoura za ta kai ziyara Saliyo"

Post a Comment