Clinton ko Trump: Amurkawa na kada kuri'a
Al'ummar Amurka na kada kuri'a domin zaben
sabon shugaba bayan yakin neman zabe mafi
zafi da aka taba yi a tarihin kasar.
Da sanyin safiya misalin karfe 06:00 ne aka fara
kada kuri'a a Gabashin kasar, sai dai tuni wasu
kauyuka a jihar New Hampshire sun riga sun
kada kuri'unsu.
Hillary Clinton da Donald Trump sun zagaye
kasar domin neman kuri'un jama'a a 'yan
kwanakin da suka gabata.
Za a fara samun sakamako a cikin daren ranar
Laraba da misalin karfe 04:00 na safe.
Duka 'yan takarar sun yi gangamin yakin neman
zabe a jihohin North Carolina da Pennsylvania da
kuma Michigan, inda nan ne takarar ta fi zafi.
Sai dai tuni Amurkawa miliyan 46 suka jefa
kuri'unsu a jihohin da suka bude rumfunan
zabensu kwanakki gabanin wannan ranar ta
zaben gama-gari.

0 Response to "Clinton ko Trump: Amurkawa na kada kuri'a"
Post a Comment