Inter ta dauki Pioli a matsayin kociyanta

Inter Milan ta nada tsohon kociyan Lazio,
Stefano Pioli, a matsayin wanda zai horar da
kungiyar.
Pioli mai shekara 51, ya saka hannu kan
yarjejeniyar da zai ja ragamar kungiyar har zuwa
Yunin 2018, zai kuma maye gurbin Frank de Boer
wanda aka sallama, bayan kwanaki 85 da ya yi
aiki.
Sabon kociyan zai fara jan ragamar kungiyar a
wasan hamayya da za ta yi da AC Milan a San
Siro a ranar 20 ga watan Nuwamba.
Shi ne kuma mai horar wa na tara da zai horar
da kungiyar tun lokacin da Jose Mourinho ya bar
Inter, bayan da ya lashe kofin zakarun Turai a
shekarar 2010.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Inter ta dauki Pioli a matsayin kociyanta"

Post a Comment