Duniya za ta shiga-uku idan aka zabi Trump - Obama

Shugaban Amurka Barack Obama ya yi kira ga
'yan jam'iyyar Democrats daga kowacce kabila
su fito su zabi Hillary Clinton, yana mai
gargadin cewa 'yan Republic da ma sauran
al'umar duniya za su shiga uku idan Donald
Trump ya zama shugaban kasar.
Obama ya ce Trump hatsari ne ga 'yancin kasar
na walwala.
Shugaban na Amurka na magana ne a wajen
yakin neman zaben Hillary Clinton jihar North
Carolina.
Sai dai Mr Trump ya ce ya kamata Mr Obama ya
daina yi wa Clinton yakin neman zabe, ya mayar
da hankali kan mulkin kasar.
Ya shaida wa magoya bayansa a Pensacola da
ke Florida cewa,"Babban batu dai shi ne babu
wanda ke son Obama ya sake mulki tsawon
shekara hudu."
Ya ce a 'yan kwanakin nan Mrs Clinton ta zama
"mahaukaciya."
A ranar Talatan makon gobe ne dai Amurkawa
za su kada kuri'unsu a zaben da ke cike da ce-
ce-ku-ce, yayin da kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta
nuna cewa 'yan takarar biyu sun yi kankankan.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Duniya za ta shiga-uku idan aka zabi Trump - Obama"

Post a Comment