Golar Gambia ta nutse a ruwa a hanyar shiga Turai

Mai tsaron ragar tawagar kwallon kafar mata ta
kasar Gambiya ta mutu bayan ta nutse a ruwa a
tekun Bahar-rum lokacin da ta ke kokarin shiga
nahiyar Turai.
Hukumar kwallon kafa ta kasar ta ce Fatim
Jawara, mai shekara 19, tana cikin wani kwale-
kwale ne da ya samu matsala a watan da ya
gabata.
Shugaban hukumar Lamin Baba ya shaida wa
BBC cewa dangin Fatim sun tabbatar da
mutuwarta.
Da dama daga cikin 'yan ciranin da ke tsallaka
wa Italiya sun fito ne daga Gambia.
Jawara ta fara buga wa kasar kwallo ne a bara,
bayan da ta taka leda a tawagar matasa ta
Gambia.
Mista Bajo ya shaida wa kamfanin dillancin
labarai na AFP cewa, "Za a iya tuna ta saboda
fanaretin da ta kade a wasan sada zumunta
tsakanin kasar da kuma Glasgow Girls na
Scotland".
Fiye da 'yan cirani da 'yan gudun hijira 3,300 ne
suka mutu a tekun Bahar-rum a bana.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Golar Gambia ta nutse a ruwa a hanyar shiga Turai"

Post a Comment