Nigeria: Mutum 700,000 na neman guraben aiki 500

Gwamnatin Najeriya ta ce ta samu fiye da masu
neman aiki dubu 700 da ke neman guraben aikin
da aka tallata na mutum 500 a hukumar tara
haraji ta kasar, FIRS.
Shugaban Hukumar Tunde Fowler ne ya bayyana
hakan ga kwamitin majalisar wakilan kasar kan
sauraron koke-koken jama'a.
Ya ce sama da mutum 2, 000 daga cikin masu
neman aikin na da digiri daraja ta daya, kuma
dukkansu sun cancanci a dauke su.
Hakan na zuwa ne a yayin da kasar ke cigaba da
fama da matsalar tatattalin arziki mafi muni cikin
shekaru.
Wannan lamari dai ya nuna yadda ake fama da
rashin aikin yi a Najeriya, kasar da ta fi kowacce
girman tattalin arziki a nahiyar Afirka.
Mutane da dama ne suka rasa rayukansu a
turmutsutsun neman aiki shekara biyu da ta
wuce a sassan kasar daban-daban.
Matasa a Najeriya dai na cigaba da fama da
rashin ayyuka, wanda hakan ke da matukar
barzana ga zaman lafiyar kasar baki daya.
Masu sharhi na ganin rashin abun hannu na daya
daga cikin dalilan da rikice-rikice kamar na Boko
Haram da mayakan Naija-Delta ke cigaba da
ruruwa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria: Mutum 700,000 na neman guraben aiki 500"

Post a Comment