Soyinka zai yaga katinsa na zama a Amurka idan Trump ya ci zabe

Shahararren marubucin nan na Najeriya, Wole
Soyinka, ya ce zai yaga katinsa na shaidar zama
a Amurka wanda ake kira green card, idan har
Donal Trump ya ci zabe.
Jaridar Guardian ta rawaito cewa Mista Soyinka
na cewa ba lallai ba ne Trump ya ci zaben, a
lokacin da yake jawabi a jami'ar Oxford da ke
Birtaniya.
Ya kara da cewa amma kuma idan har ya ci, to
abu na farko da zai fada shi ne "duk masu katin
shaidar zama a Amurka na green card sai sun
sake neman izini".
Jaridar ta ambato shi yana cewa "to ni ba zan
jira wannan ba".
Ya kara da cewa "Da zarar sun sanar da nasarar
shi, zan yaga kati na da kai na, sannan na fara
tattara kayana".
Mista Soyinka dai malami ne a cibiyar nazari kan
harkokin Afirka da Amurka da ke jami'ar New
York.
Shi ne mutumin Afirka na farko da ya samu
lambar yabo na Nobel a kan rubutun adabi a
shekarar 1986.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Soyinka zai yaga katinsa na zama a Amurka idan Trump ya ci zabe"

Post a Comment