Hong Kong: China ta hana wdansu 'yan majalisa kama aiki

Kasar China ta dauki matakai na ba-zata a kan
harkokin siyasar yankin Hong Kong na hana
wadansu 'yan majalisa biyu kama aiki.
'Yan majalisar masu goyon bayan samun 'yancin
cin-gashin kai, Sixtus Leung da Yau Wai-ching,
sun ki amincewa su yi mubaya'a ga kasar China
a yayin rantsar da su.
Chinar na yi wa wani bangare na dokar Hong
Kong iyakar cewa, duk wani jami'i da bai sha
cikakkiyar rantsuwar kama aiki ba za a haramta
masa shiga ofis, kamar yadda wata kafar yada
labarai a kasar ta bayyyana.
Matakin na zuwa ne bayan rudanin da aka shafe
makonni ana yi a majalisar dokokin kasar ta
Hong Kong.
'Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa
kwalla wajen tarwatsa masu zanga-zangar a
wajen ofishin hulda da jama'a na yankin Hong
Kong, tare da cafke akalla mutane hudu.
Yankin Hong Kong yanki ne mai cin gashin kai a
wasu bangarorin a karkashin kasa guda, amma
kuma a bisa tsare-tsaren mulki biyu tun bayan da
ya koma China a shekara ta 1997.
Amma kuma a kundin tsarin mulkin yankin, da
muhimman dokoki sun tanadi cewa kasar China
ce za ta rika bayar da shawara ta karshe a kan
yadda za a yi amfani da dokokin.
Yankin na Hong Kong na kallon katsalandan din
kasar China a matsayin wani babban kalubale ga
'yancin fadin albarkacin baki da na harkokin
shari'a.
Ana kuma kallon duk wani batu kan 'yancin cin-
gashin kai a matsayin wata barazana.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Hong Kong: China ta hana wdansu 'yan majalisa kama aiki"

Post a Comment