Wani Matashi a Kano ya hada mota mai amfani da hasken rana

Wani matashi a birnin Kano na arewacin
Najeriya ya kirkiri wata mota mai amfani da
makamashin hasken rana a maimakon man
fetur.
Matashin, Mukhtar Adamu Fasaha, dan shekara
23 ya ce motar, wadda ta yi tafiyar sama da
kilomita 1 a wani gwaji da ya yi, an hada ta ne
da karafa da katakai da batur da faifan zuko
hasken rana.
Ya ce faifan, wanda ya yi wa motar rumfa, shi
ne yake bai wa batirin motar wuta.
Tana kuma amfani da wani moto irin na injin
jawo ruwa wanda yake samun wuta daga
batirinta, sannan ya juya kundun giya, ta yadda
tayoyinta za su fara tafiya.
An sanya wa motar kundun giya da tayoyin babur
Vespa, kuma ana iya inganta fasahar wajen rage
dogaro da man fetur zuwa amfani da makamashi
maras gurbata muhalli, don harkokin sufuri a
kasashen Afirka kamar Nijeriya.
A cewar matashin, idan akwai kayan aiki, ana iya
inganta ta, a fadada ta, a musanya katakan da
ke jikinta da karfe yadda za ta fi karko da jan
hankali.
Mukhtar ya kuma ce ya shafe kimanin shekara
biyu yana tara kayan hada motar, amma a cikin
kwana 11 ya hada ta.
"Akwai abubuwan da za a iya saukaka ta'ammali
da man fetur din kamar irin wadannan (motoci)
in aka yi su manya-manya haka. Ka ga an samu
sauki ma ke nan", inji shi.
Motar mai fadin inci 40 da tsawon inci 72 tana
da mazaunin mutum biyu ne amma matashin ya
ce tana da karfin daukar mutum hudu. Ya ce ya
sayi kayayyaki da dama, wasu kuma ya tsince su
don hada wannan mota da ke iya tafiya har ma
da baya da baya.
An sauya fasalin moto dinta daga ainihin karfin
voltage 480 da yake da shi zuwa voltage 360 ko
240 ta yadda batirin da aka sa mata zai iya
dadewa yana aiki ba tare da ya ja lantarki mai
yawa ba.
Matashin ya ce idan aka sa wa motar
ingantaccen batir mai karfi zai iya ba ta wutar da
za ta yi gudu a lokaci guda kuma ta adana wani
bangare na lantarki ko da za a shiga yanayin da
ba hasken rana.
Ya kuma ce an tsara fasahar motar ce yadda ba
za ta dinga fitar da hayaki ko yin wata k'ara ba,
amma saboda ba a goge kacar da aka sanya
mata ba, tana yin guga.
Ya zuwa yanzu ba a tantance gudun kilomita
nawa take iya yi a cikin sa'a guda ba, amma dai
makerin motar ya ce zai yi hakan a nan gaba
idan ya sauya mata batir.
Da haka kasashe suke cigaba
Najeriya na da dumbin hazikan matasa irinsu
Mukhtar Fasaha masu kirkirar abubuwa iri daban-
daban, sai dai ba su cika samun tallafi don
bunkasa irin wadannan fasahohi na cikin gida ba.
Makerin motar ya ce da tallafa wa mutane masu
fasahar kirkire-kirkire kasashe suke ci gaba.
A cewarsa, idan aka tallafa to kasa za ta rika
kirkirar abubuwa nata na kanta, ba sai ta dogara
an shigar mata da wasu abubuwa daga waje ba.
"Rashin kudi ya hana ni cigaba da karatu"
Mukhtar Fasaha, wanda ya ce rashin samun
tallafi ya hana shi ci gaba da karatu, ya halarci
makarantar firamare ta Maimuna Gwarzo a
Kaduna. Daga nan ya wuce zuwa karamar
makarantar sakandaren Digital Science, kafin ya
koma Kano wajen mahaifinsa a shekara ta 2010.
Ya ce yana gyaran rediyo da wayar salula, kuma
ya taba kera taransimitar rediyo har ma ya dinga
yada shirye-shirye kuma ya hada inverter ta gida.
Matashin ya ce a yanzu haka shi yaron shago ne
a kasuwar Kantin Kwari.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Wani Matashi a Kano ya hada mota mai amfani da hasken rana"

Post a Comment