Nigeria ta aike da 'yan sanda mata sansanonin 'yan gudun hijira

An aike da 'yan sanda mata 100 a sansanonin
'yan gudun hijira a jihar Borno da ke arewa maso
gabashin Nigeria.
Najeriya ta dauki matakin ne bayan wata
kungiyar masu fafutuka ta zargin jama'ian tsaro
maza da cin zarafin mata da kananan yara.
Shugaban 'yan sanda na jihar, Damian Chukwu
ya ce an dauki matakin ne domin karfafa gwiwar
dubban mata da kananan yara mata da ke
sansanonin.
Ya kara da cewa " muna ganin cewa matan ba
za su saki jiki suyi magana da maza ba, amma
zasu samu kwarin gwiwar bayyana wa 'yan sanda
mata idan har ya kasance zargin da ake yi
gaskiya ne".
Shugaba Muhammadu Buhari dai ya bukaci a yi
bincike a kan batun ne bayan kungiyar kare
hakkin bil adama ta Human rights Watch ta ce ta
yi magana da mata 43, wadanda jami'an tsaro ko
kungiyar 'yan banga suka yi wa fyade ko suka ci
zarafinsu.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria ta aike da 'yan sanda mata sansanonin 'yan gudun hijira"

Post a Comment