Toni Kroos zai yi jinya

Likitocin Real Madrid sun tabbatar da cewar dan
kwallon tawagar Jamus, Toni Kross, ya yi rauni.
Dan kwallon ya yi rauni ne a karawar da Madrid
ta ci Leganes 3-0 a ranar Lahadi a gasar La Liga
da suka fafata.
A makon jiya ne, Toni Kross, ya sabunta
yarjejeniyarsa da Real Madrid domin ci gaba da
buga mata tamaula zuwa 2022.
Dan kwallon mai shekara 26, wanda ya koma
Bernabeu daga Bayern Munich a shekara 2014,
ya ci wa Madrid kwallaye hudu a wasanni 108 da
ya buga mata

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Toni Kroos zai yi jinya"

Post a Comment