Iska mai gurbata muhalli ta sa an kulle makarantu a Delhi

Ministan Delhi na kasar India ya sa an kulle
dukkan makarantun birnin tsawon kwana uku a
yayin da mazauna birnin ke fama da iska mai
gurbata muhalli.
Arvind Kejriwal ya bayyana hakan ne bayan wani
taron gaggawa da ya gudanar da masu ruwa da
tsaki, yana mai shan alwashin shawo kan
matsalar.
Yanzu haka dai an dakatar da dukkan ayyukan
gine-gine da rushe-rushe a birnin har kwana
biyar.
Za a feffesa ruwa a kan manyan titunan birnin
domin kwantar da kurar da ke damun mutane.
Mr Kejriwal ya bayar da shawara ga mazauna
binrin na Delhi da su yi zamansu a cikin
gidajensu kana ma'aikata su yi ayyukansu a gida
idan da dama.
Kazalika gwamnati ta sanar da cewa za a kashe
wutar da ake kunnawa a kamfanonin fada dutse,
sannan a rufe tashar samar da ma'adinin kwal da
ke Badarpur.
Tun ranar Asabar ne dai aka rufe makarantu
1,800 na kwaryar birnin saboda iska mai gurbata
muhalli.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Iska mai gurbata muhalli ta sa an kulle makarantu a Delhi"

Post a Comment