An kama mutane 16 da suka buya a jirgi don zuwa Amurka

 Jami'an sashen bincike da kuma ceto na
hukumar kula da tashohin jiragen ruwan Najeriya
tare da sojojin ruwa na kasar sun kama wasu
mutane 16 da suka shiga kuma suna buya a
cikin wani jirgin ruwa mai niyyar zuwa Amurka.
An kama mutanen da suka hada da dan kasar
Liberia guda ne a kusa da gabar ruwan babban
birnin kasuwancin kasar wato Legas.
Wata sanarwa daga mai magana da yawun
hukumar ta tashoshin jirage ruwa wato NIMASA,
Hajiya Lami Tumaka, ta ce an kama mutanen ne
bayan da matukin jirgin ya aike da wani sakon
neman dauki zuwa ga cibiyar tsara bincike da
kuma aikin ceto ta hukumar wadda ita kuwa ta
sanar da sojan ruwan Najeriya.
Ta ce daya daga cikinsu ya samu rauni a kafada
lokacin da yake kokarin tserewa amma jami'an
aikin ceto na hukumar sun garzaya da zuwa
asibiti domin yi masa magani, yayin da jami'an
sojin ruwan suka yi awon gaba da sauran
mutanen 15 domin daukar bayanansu da kuma
mika su ga hukumomin tsaro domin ci gaba da
bincike.
Matuka jirgin na MV Colombia River wanda aka yi
wa rijista a tsibirin Hong Kong, sun ce da farko
sun zaci cewa 'yan fashin teku ne suka kawo
musu farmaki, amma binciken farko-farko ya
nuna cewa mutanen masu kutse ne kawai da
suka so bin jirgin zuwa kasar Amurka domin
neman abin yi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An kama mutane 16 da suka buya a jirgi don zuwa Amurka"

Post a Comment