Jam’iyyar PDP za ta hade da wasu ‘Yan adawa

Jam’iyyar PDP na kokarin hadewa da
sauran wasu Jam’iyyun adawa na Kasar
– Shugaban Bangaren Jam’iyyar PDP
Ahmad Makarfi ya kafa wani kwamiti da zai
duba wannan hadaka
– Jam’iyyar PDP na kokarin karbe mulki
daga hannun Jam’iyyar APC-mai mulki
Ahmed Makarfi na Jam’iyyar PDP
Jam’iyyar PDP mai adawa, na kokarin ganin
ta karbe mulkin Kasar nan daga hannun APC
zuwa shekarar zabe 2019. Shugaban wani
Bangaren na PDP, Ahmed Makarfi ya nada
wani Kwamiti da zai fara wannan shiri.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Ahmad
Makarfi ya nada wani kwamiti mai dauke da
mutane 115 da za su zauna suyi aiki da
sauran Jam’iyyun adawa na Kasar wajen
ganin sun karbe mulki daga hannun
Jam’iyyar APC. Ahmad Makarfi yace sun
fara shirin ganin cewa sun dawo mulki nan
da zabe mai zuwa.
Ahmad Makarfi yace Kwamitin tayi kokarin
bin duk hanyar da ta dace na hada kai da
sauran Jama’a wajen dawowa mulkin Kasar
domin ceto Najeriya da Damokaradiyya.
Jam’iyyar PDP tace za tayi garambawul ga
tsarin mulkin ta wajen ganin an ci wannan
manufa.
An dai nada tsohon Ministan yada labarai na
Kasar, Farfesa Jerry Gana ne a matsayin
Shugaban Kwamitin. Jam’iyyar PDP tace
lokaci fa na tafiya, don haka sai an dage.
Jam’iyyar PDP, watakila ta hada kai da
sauran Jam’iyyu kamar yadda APC mai mulki
tayi a baya wajen buge PDP daga mulkin
Kasar bayan shekara da shekaru tana mulkin
Kasar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Jam’iyyar PDP za ta hade da wasu ‘Yan adawa"

Post a Comment