Yadda Trump ya bai wa duniya 'ruwa'

Zaben da aka yi wa Donald Trump a matsayin
shugaban Amurka ya bai wa wasu mutane
mamaki ganin yadda aka yi hasashen cewa ba
zai kai labari ba.
Kuri'ar jin ra'ayin mutane a Amurka ta nuna
cewa 'yar takarar shugabancin kasar karkashin
jam'iyyar Democrat, Hillary Clinton ta ba wa
abokin hamayyarta na jam'iyyar Republican,
Donald Trump, tazara a ranar jajiberin fara zabe.
Wannan dai bai zo wa mutane da mamaki ba
ganin cewa a duk lokacin da aka gudanar da irin
wadannan kuri'un na jin ra'ayin mutane a
watanni shidan da suka gabata, alkaluma sun sha
juya wa Donald Trump baya ko da kuwa sun
nuna shi ne ya yi wa Hillary Clinto zarra da
farko.
Da alama dai al'ummar Amurka ba za su so
ganin Donald Trump yana shugabantar su ba
kuma a duk lokacin da sa'a ta karkata wurin
Trump, masu fada aji a harkar zaben kasar suna
iya bakin kokarinsu wajen dakile hakan.
To idan dai wannan ne abin da ke faruwa a
Amurka a yanzu haka, to da alama Hillary Clinton
ce za ta lashe zaben shugaban kasar.
Sai dai kuma wani abu dangane da kuri'ar jin
ra'ayin mutanen shi ne, ba a ji ra'ayin masu zabe
ba kan martanin da suke mayarwa game da
wankewar da Hukumar FBI ta yi wa Clinton ba
dangane da batun goge dubban sakonnin imail da
aka ce ta yi.
To amma wani abu shi ne, cin zabe a Amurka ba
abu ne da ake la'akari da yawan kuri'ar da 'yan
kasa suka kadawa mutum ba.
Hakan na dogara ne da yawan johohin da mutum
ya lashe da za su ba wa dan takarar damar lashe
manyan mazabu 270.
Saboda haka, sakamakon kuri'ar jin ra'ayin
mutanen da aka gudanar a baya-bayan nan ya
nuna cewa har yanzu Donald Trump zai iya cin
zabe.
To amma fa dole ne sai 'yan jam'iyyar
Republican din sun tashi tsaye wajen lashe
mazabu a jihohi kamar Pennsylvania da Michigan
da kuma Virginia, a inda Clinton take jan ragama.
Shi dai Mista Trump yana da dimbin masu goyon
baya a tsakanin farar fata masu fada aji, a inda
ita kuma Clinton take da masu mara mata baya
masu yawa a tsakanin bakake da matasa.
Har wa yau, Donald Trump ba zai sakankance da
irin yadda Hispaniyawa suka yi fitar farar dango
wajen kada kuri'a ba duk kuwa da cewa shi ne
mutumin da ya zaburar da su domin su fita su
kada kuri'ar.
Sai dai fa sakamakon wa suka zaba sai an je
kidaya tukunna.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Yadda Trump ya bai wa duniya 'ruwa'"

Post a Comment