Kasashen duniya sun mayar da martani kan zaben Trump

Kasashen duniya sun soma mayar da martani
kan zaben da Amurkawa suka yi wa Donald
Trump a matsayin sabon shugaban su.
Kasar Turkiya ta yi maraba da Trump, kodayake
ya yi kira a gare shi da ya mika masa Fethullah
Gulen, Malamin nan dan Turkiyya wanda ke
zaune a Amurka saboda zargin da ake yi masa
na kitsa juyin mulkin da aka yi yunkurin yi a
kasar a watan Yuli wanda bai yi nasara ba.
Shi ma shugaban Tanzania, John Magufuli ya
taya shugaban Amurka mai jiran gado murnar
nasarar da ya samu, yana mai ba shi tabbacin ci
gaba da kawance tsakanin kasashen biyu.
A nasa bangaren, shugaban kasar Philippine
Rodrigo Duterte ya yi san-barka ga Donald
Trump.
Wani ministan kasar ya ambato Duterte na cewa
"Yana sa ran yin aiki tare da sabuwar gwamnatin
domin inganta dangantaka tsakanin Philippines
da Amurka ta hanyar mutunta juna da cin gajiyar
juna da kuma tabbatar da dimokradiyya da mulki
na gari a tsakanin mu."
Shi ma Firai Ministan New Zealand John Key ya
taya Mr Trump murna, yayin da takwaransa na
Australia Malcolm Turnbull ya ce Amurkawa "sun
fahimci cewa ba su da aminai kamar 'yan
Australia".

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Kasashen duniya sun mayar da martani kan zaben Trump"

Post a Comment