Hari ta sama ya kashe mutum 16 a Raqqa

Harin saman gamayyar rundunar kawancen da
Amurka ke jagoranta ya yi sanadin mutuwar
akalla farar hula 16 a wani kauye a arewacin
Raqqa na Syria inda 'yan kungiyar IS ke da
karfin iko, a cewar masu fafutika.
Kungiyar kare hakkin bil adam ta Burtaniya da ke
da cibiya a Syria ta rawaito cewa mata 6 da
wani yaro na cikin wadanda suka rasa rayukansu
a harin da aka kai a al-Heisha cikin dare.
Gamayyar mayakan Kurdawa da Larabawa
wadanda Amurka ke mara wa baya, wadanda ke
son kwace Raqqa na kai hari kan kauyen da ke
karkashin ikon kungiyar IS.
Gamayyar rundunar kawancen ta ce tana duba
rahotanni kan lamarin.
Mai magana da yawun kungiyar gamayyar
kurdawa da larabawa ta yi watsi da batun.
Jihan Sheikh Ahmed ta gaya wa kamfanin
dillancin labarai na AFP cewa, "Babu wani abu
makamancin haka da ya faru, kuma duk wanda
ya yi irin wannan ikirari, to labarin IS kawai yake
bayarwa."

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Hari ta sama ya kashe mutum 16 a Raqqa"

Post a Comment