Kofin Europa: Fernebahce ta doke Man United 2-1

Fernebahce ta doke Manchester United 2-1 a
karawar da suka yi ta biyu ta kofin Zakarun
Turai na Europa wasan mako na hudu na rukunin
farko.
Kungiyar ta birnin Istanbul ta fara daga ragar
bakin nata ne a cikin minti biyu kacal da shiga fili
ta hannun dan wasanta Sow, wanda ya
shammaci 'yan Unitd din ya yi kwance-kwance
da baya ya sheka musu ita a raga.
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne kuma
a minti na 59 J. Lens ya kara kwallo ta biyu a
ragar Manchester United.
Wayne Rooney ya rama wa Man United din
kwallo daya ana dab da tashi daga wasan a minti
na 89.
Kwallon ta Rooney ita ce ta 38 da ya ci a gasar
Zakarun Turai, wadda ta sa ya kamo Ruud van
Nistelrooy a matsayin wanda ya fi ci wa United
kwallo a gasar Zakarun Turai.
Sakamakon ya sa United ta zama ta uku a
rukunin na farko (Group A), da maki daya a
bayan Feyenoord da Fenerbahce.
Kuma hakan ya jefa ta cikin hadarin kasa zuwa
mataki na gaba na sili-daya-kwale, na gasar ta
kofin Europa.
Wasa biyu ya rage wa kungiyar ta Premier, inda
za ta kara a Old Trafford da Feyenoord ta
Holland, sannan kuma ta je Ukraine ta hadu da
Zorya Luhansk.
A karawarsu ta farko mako biyu da ya gabata
Manchester United ta ci Fernebahce 4-1 a Old
Trafford.
A daya karawar da ka yi ta rukunin na daya
Zorya Luhansk da Feyenoord sun yi canjaras 1-1.
Ga sakamakon wasu daga cikin wasannin na
ranar Alhamis gguda 24:
Astana 1 - 1 Olympiakos Piraeus
Athletic Club 5 - 3 Genk
Sassuolo 2 - 2 Rapid Wien
Austria Wien 2 - 4 Roma
Astra 1 - 1 Viktoria Plzeň
Zenit 2 - 1 Dundalk
Maccabi Tel Aviv 0 - 0 AZ
APOEL 1 - 0 Young Boys
Fenerbahçe 2 - 1 Manchester United
Zorya 1 - 1 Feyenoord
Qabala 1 - 2 Saint-Étienne
Anderlecht 6 - 1 Mainz 05

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Kofin Europa: Fernebahce ta doke Man United 2-1"

Post a Comment