Nigeria: An dakatar da alkalai 7 da ake zargi da cin hanci

Hukumar da ke sa ido kan al'amuran shari'a a
Najeriya NJC ta dakatar da wasu manyan alkalai
bakwai daga gudanar da aikin alkalanci bayan da
hukumar tsaron farin kaya wato DSS ta zarge su
da karbar cin hanci da rashawa.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da direktan
yada labarai na hukumar Soji Oye ya fitar a
karshen wani taron da hukumar ta gudanar a
Abuja.
Hukumar ta NJC ta ce an dakatar da alkalan ne
har sai an kammala yi musu shari'a kan zargin
aikata cin hanci da hukumar tsaro ta farin kaya,
wato DSS ke musu bayan dirar mikiyar da ta yi a
gidajen alkalai a sassan kasar daban-daban na
kasar, inda ta kama su.
Matakin da NJC ta dauka dai ya zo ne bayan
kiraye-kirayen da Kungiyar lauyoyi ta kasar ta yi
na neman a dakatar da alkalan, tana mai cewa
hakan ya zama wajibi matukar hukumar ta na so
kimarsu ta dawo a idanun 'yan Najeriya.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria: An dakatar da alkalai 7 da ake zargi da cin hanci"

Post a Comment