Gwamnatin Nigeria za ta kara wutar lantarki

Gwamnatin Najeriya ta cimma yarjejeniya da
wasu hukumomi domin samar da karin megawat
500 na wutar lantarki a kasar.
Wannan yarjejeniya, kamar yadda mahukunta ke
cewa, za ta taimaka wajen bude wa wasu
kamfanoni ido wajen zuba-jari a bangaren samar
da makamshi a kasar.
Najeriya ta ce an cimma yarjejeniyar ce da
kamfanoni da kuma wasu hukumomi irin su
kamfanin samar da wutar lantarki na yankin
Niger-Delta, wato Niger Delta Power Holding
Company, tare da agajin Bankin Duniya.
Wata sanarwar da ofishin mataimakin shugaban
kasar ta fitar ta ce yarjejeniyar tana da matukar
muhimmanci, saboda za ta habaka harkar samar
da makamashi a kasar.
A cewar sanarwar, Kamfanin Seven Energy da ke
samar da iskar gas ya dukufa wajen zuba-jarin
da ya kai dala miliyon 500 don gina cibiyar
sarrafa iskar gas a jihar Akwa-Ibom.
Bankin Duniya zai tsaya wa kamfanin Niger-Delta
Power Holding Company a kokarin da yake yi da
kamfanin Seven Energy don sarrafa iskar gas din
zuwa wutar lantarki a wata cibiya da ke Calabar,
babban birnin jihar Cross-River.
Najeriya dai na fama da matsalar karancin wutar
lantarki, kasancewar a halin da ake ciki, wutar da
take samarwa bai kai megawatt 4000 ba.
Ga ta kuma da yawan al`umar da ta kai miliyon
180, wadda masana ke cewa tana bukatar ninkin
baninkin wutar da gwamnati ke samarwa yanzu,
kafin a kai ga gamsar da al`umar kasar.
Gwamnatocin da suka gabata dai sun dauki
matakai daban-daban da nufin inganta wutar
lantarki a kasar.
Wannan ya kama daga sauya wa hukumar wutar
kasar sunaye iri-iri, zuwa sayar da hannayenn-
jarinta ga wasu da aka ce `yan kasuwa ne.
Amma har yanzu ba ta sauya zani ba,
sakamakon zargin da ake yi na cin hanci da
kuma matsalar hare-haren da `yan bindiga ke
kaiwa kan bututan da ke samar da iskar gas a
yankin Niger Delta.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Gwamnatin Nigeria za ta kara wutar lantarki"

Post a Comment