Toure ya bayar da kai bori ya hau

Dan wasan tsakiya na Manchester City Yaya
Toure ya nemi gafarar kungiyar "saboda
abubuwan da suka faru a baya".
Kocin City Pep Guardiola ya ce ba zai sanya
Toure, mai shekara 33 a wasa ba, sai lokacin da
wakilinsa Dimitri Seluk ya nemi gafara a kan
sukar da ya yi masa saboda kin sanya dan
kwallon a jerin 'yan wasan da ke buga gasar
zakarun turai.
Sai dai a wani sako da ya wallafa a shafinsa na
Facebook, Toure, ya ce "Ina neman gafara - a
madadi na da wadanda ke wakilta ta."
Ya kara da cewa "Ba a fahimci kalaman da aka
yi ba, don haka ba sa nuna akwai matsala
tsakanina da kulob dina."
Seluk ya ce an wulakanta Toure saboda rashin
sanya shi a cikin tawagar da ta buga gasar
zakarun turai.
Shi kuma kocin City ya ce: "Ba zan lamunci
yanayin da dan wasa zai caccake ni a kafafen
watsa labarai ba saboda ban sanya shi a wasa
ba."
Toure, wanda bai buga wa City wasa ba tun
ranar 24 ga watan Agusta, ya kara da cewa :
"Ina matukar mutunta Manchester City kuma ina
yi wa kulob din fatan alheri."
Ya kara da cewa: "Ina matukar alfahari da na
buga wa kulob din wasa kuma ina son taimakon
sa domin ya ci gaba da yin nasara. Zan ci gaba
da buga kwallo domin na burge 'yan kallo."

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Toure ya bayar da kai bori ya hau"

Post a Comment