Yaki da cin hanci: Oba na Benin ya yabawa Shugba Buhari

– Oba na Benin ya yabawa Shugaba Buhari
da aikin da yake yi
– Oba na Benin yace Shugaba Buhari na
kokari wajen fada da cin hanci a Kasar nan
– Sabon Sarkin ya kuma godewa Shugaba
Buhari da mutanen na su da ya nada a
Gwamnatin sa
Mai Girma Oba na Benin, Omo n’Oba n’Edo
Uku Akpolopkolo Oba Ewuare II ya yabawa
Shugaba Buhari wajen yaki da cin hanci da
rashawa a Kasar nan. Sabon Sarkin Oba
Ewuare na Biyu yace Shugaba Buhari yana
taka rawar gani a wajen wannan aiki.
Oba na Benin yace Shugaba Buhari ya nuna
bajinta wajen rike Kasar duk da cewa ana
fama da rashin arziki. Oba na Benin din ya
bayyana hakan ne yayin da Shugaba Buhari
ya kai masa ziyara, a jiya. Shugaban Kasar
ya je Garin Benin din ne kaddamar da
ayyukan Gwamna Oshiomole mai barin gado.
Shugaba Buhari ya taya Sabon Sarkin murna,
wanda shine Oba ne Benin na 40 a Jerin
sarautar. Shugaba Buhari ya tunawa Jama’a
cewa ya zauna a wannan gari na wata da
watanni . Buhari yace: Mutane da dama ba su
san na zauna a wannan Gari ba har na
watanni 40 a wani dan karamin gida, bayan an
yi mani juyin mulki a shekarar 1985.
Oba na Benin din ya godewa Shugaba Buhari
da ya nada mutanen su a Gwamnati, ya
kuma roki Shugaba Buhari da ya gyara
Yankin Gelegele na Jihar Edo.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Yaki da cin hanci: Oba na Benin ya yabawa Shugba Buhari"

Post a Comment