Tsarin tekunan duniya da abubuwan da ke cikinsu (1)
Matashiya
Idan masu karatu ba su manta ba, a baya mun
fara bayani kan tekunan duniya da irin abubuwan
da ke cikinsu (ko karkashinsu), inda muka yi
bayani kan tekun Pacific, wanda shi ne babba,
mafi fadi da girma a duniya. Bayan tekun Pacific
mun fara bayanai kan teku na biyu da ke biye da
shi, wato tekun Atlantika, ko “Tekun Legas,”
kamar yadda muka saba kiransu a Najeriya. A
karkashin wannan gaba dai mun gabatar da
kasidu guda biyu.
Na farko kan asali da samuwar tekun Atlantika,
inda muka duba bangaren tarihi da kuma bagiren
da wannan teku yake a duniya. Sannan a karshe
muka sanar da mai karatu cewa Turawa sun
dade suna gudanar da bincike na kimiyya kan
sha’anin teku a wannan bagire tun sama da
shekaru dari da suka gabata. A kasida ta biyu
kuma mun jero bayanai ne kan tarihin tafiye-
tafiyen bude ido da burgewa da Turawa suka yi
ta yi, har zuwa wannan karni da muke ciki. A
yau cikin yardar Allah, ga shi mun dawo don ci
gaba da bayani kan tekun Atlantika. Za kuma mu
dubi tasirin wannan teku ne wajen ci gaban
tattalin arzikin kasashen duniya da kuma
sadarwa.
Tasiri Wajen Tattalin Arzikin kasa
Kamar yadda bayanai suka gabata, tekun
Atlantika babban teku ne. Shi ne na biyu a
duniya, sannan ya hada alaka tsakanin manyan
nahiyoyin duniya guda uku; nahiyar Amurka
(Kudanci da Yammaci) ta bangaren
yammacinsa. Sai nahiyar Afirka daga bangaren
Arewaci. Nahiyar Afirka na daga cikin nahiyoyin
da suka fi yawan jama’a a duniya. Sai kuma
nahiyar Asiya ta gabashinsa, inda ya jonu da
tekun Indiya (Bahar Maliya) daga gabas, ya
nausa can don hadewa da shi.
Wannan gamayyar manyan nahiyoyin duniya da
tekun Atlantika ya hada ya taimaka wajen
saukake hanyoyin kasuwanci a tsakanin
kasashen duniya. Tekun Atlantika wani babban
titi ne na kasuwanci, inda manyan jiragen ruwa
ke dauko dukiyoyin kasuwanci da hajoji nau’uka
daban-daban daga nahiyar Amurka zuwa Afirka.
Haka ma sukan dauko kayayyaki daga nahiyar
Amurka zuwa nahiyar Asiya, kai tsaye ko ta
hanyar yin Zango a nahiyar Afirka. Bayan
wannan, har wa yau jiragen kasuwanci kan taso
daga nahiyar Amurkan dai zuwa nahiyar Turai;
musamman masu tasowa daga bangaren Latin
Amerika (Kudancin Amurka - South America).
A daya bangaren kuma, jiragen ruwan kasuwanci
kan nausa daga nahiyar Afirka zuwa nahiyar
Asiya, daga can kusa karasa Turai, ta hanyar
maliya da ke sada su da tekun Pacific. A wasu
lokuta kuma akwai masu tashi daga Afirka zuwa
nahiyar Amurka kai tsaye, don kaiwa da daukowa
ko kaiwa da dawowa; ya danganci abin da ya
sawwaka.
Wannan jele da jiragen ruwan kasuwanci ke yi
tsakanin wadannan nahiyoyin duniya ta cikin
tekun Atlantika ya taimaka gaya wajen habaka
dangantakar kasuwanci tsakanin ma’abota
wadannan wurare. Wannan kuma, a Turance, shi
ake kira: “Transatlantic Trade,” a zamanin yau.
Akwai tashoshin jiragen ruwa a dukkan kasashen
da ke gaba da wannan teku a duniya baki daya;
tsakanin Afirka, da Asiya, da kuma nahiyar
Amurka.
A karkashin wannan teku mai albarka, akwai tarin
albarkatun kasa irin su Man Fetur da ke makare
cikin curarrun duwatsun da ke karkashin tekun.
Akwai sinadaran Gas, da duwatsun gini da kuma
duwatsun alfarma a jibge a karkashin wannan
muhalli. Bayan wadannan, an gano tarin
duwatsun zinare a nisan zurfin da bai shige mil
daya ba, a karkashin tekun. Bincike ya nuna
cewa, gano hanyoyin zakulo wadannan duwatsun
zinare a halin yanzu ba abu ba ne mai sauki, idan
an yi la’akari da yanayin muhallin. Sai dai nan
gaba.
Bayan haka, tekun Atlantika ne ke dauke da
albarkatun kifi mafi girma a duniya; fiye da tekun
Pacific ma. Wuraren da suka fi kowane tarin
wannan nau’in albarkar kifaye su ne: bakin
tsibirin Newfoundland da Dogger Bank da ke
kasar Scotland, sai Georges Bank na kasar
Amurka, da kuma tsibirin Bahamas.
Tasiri Wajen Sadarwa
Masu karatu za su yi mamakin jin cewa tekun
Atlantika wata matattara ce da ke dauke da
hanyoyin sadarwa. Kusan dukkan manyan
kamfanonin sadarwa na duniya, da gidajen yanar
sadarwa na duniya, da gwamnatocin kasashe
daban-daban (ta hanyar kamfanoni
hukumominsu), sun binne wayoyin sadarwa
nau’in “Fiber Optics,” wanda hadakar waya ce,
amma a yanayin gilashi, mai daukar siginar
bayanan sadarwa na zamani cikin mafi saurin
yanayi da girma.
A halin yanzu an kiyasta cewa, kashi 95 cikin 100
na a kalla na hanyoyin sadarwa na zamani suna
amfani ne da wayoyin sadarwa na “Fiber Optics”
ta karkashin teku, don aiwatar da sadarwa. A
yayin da ragowar ke amfani da tsarin sadarwa ta
wayar-iska (Wireless). Wannan ya faru ne
saboda ingancinsa da kuma sauri wajen aikawa
da sakonnin bayanai na zamani. A yayin tsarin
hanyar aikawa da sakonni ta wayar-iska ke
daukar mizanin bayanai biliyan daya cikin dakika
guda (1GB per second), tsarin aikawa da sakonni
ta wayar “Fiber Optics” na daukar mizani tiriliyon
daya ne a duk dakika guda (1Terabyte per
second). Wacce alakar ce wannan da tekun
Atlantika?
Alakar ta samo asali ne saboda mahalli. Ma’ana,
kusan dukkan madaukan wadannan bayanai suna
biyowa ta cikin wasu wayoyi na sadarwa da aka
shimfide su a karkashin tekunan duniya, ciki har
da tekun Atlantika. Sai dai ba yau abin ya fara
ba.
Yunkurin farko da aka fara yi wajen shimfide
wayoyin sadarwa a karkashin teku dai ya faro ne
tun cikin shekarar 1850s. Malaman tarihi suka
ce a lokacin ne aka fara shimfida wayoyi masu
dauke da siginar sadarwa don amfani da na’urar
“Telegraph.” Hakan ne ya saukake tare da bayar
da damar karba da iya aika sakonni tsakanin
nahiyoyin duniya masu dauke da wannan na’ura.
Duk da cewa a lokacin kusan kasashen
yammacin duniya ne kadai ke mallakar wannan
na’ura ta “Telegraph,” to amma ganin cewa suna
mulkin mallaka a lokacin, kuma hukumominsu sun
yadu tsakanin tsakiya zuwa gabashin duniya da
kuma nahiyar Afirka, sai suka yi wannan kokari
don samun damar aikawa da sakonni cikin
gaggawa daga kasashensu zuwa inda suke
mulkin mallaka ko akasin hakan.
Sai yunkuri na biyu, wanda ya samu bayan
gushewar na’urar “Telegraph,” sanadiyyar
samuwar na’urar wayar tangaraho. Shi ma ya
haddasa shimfide wayoyin sadarwa masu dauke
da siginar rediyo don daukar murya daga wata
nahiya zuwa wata. Daidai wannan lokaci dai
duniyar ta fara gamewa a fannin sadarwa,
sanadiyyar yaduwar wayoyin tangaraho irin na
zaman baya (Analog).

0 Response to "Tsarin tekunan duniya da abubuwan da ke cikinsu (1)"
Post a Comment