Nigeria: Ana cacar baki kan karbo rancen $30bn

A Najeriya, babbar jam`iyyar adawar kasar wato
PDP da wasu kungiyoyi sun ce ba sa goyon
bayan shirin gwamnatin kasar na karbar rancen
dala biliyon 30.
Gwamnatin dai na son karbo rance ne don cike
gibin kasafin kudin kasar na shekara uku tare da
aiwatar da wasu ayyukan inganta rayuwar
jama`a.
Sai dai jam`iyyar adawa ta PDP ta ce kamata ya
yi shugaba Buhari ya yi amfani da kudaden da
gwamnatinsa ke ikirarin ta kwato daga hannun
wasu da aka samu laifin sama da fadi da
kudaden gwamnati wajen cike gibin kasafin
kudin.
Sai dai jam`iyyar APC mai mulki ta ce PDP ta fi
kowa sanin wadanda suka wawure kudaden
kasar kuma ya kamata ta taimaka wajen kwato
kudaden.
A ranar Talata ne majalisar dattawan kasar ta yi
watsi da bukatar shugaban Buharin ta karbar
rancen dala biliyon 30 daga waje don cike gibin
kasafin kudin kasar na shekaru uku masu zuwa
saboda ba a yi musu bayani a kan sharudan da
ke tattare da bashin ba.
Sai dai mai taimaka wa shugaban kasar a kan
harkokin majalisar wakilai, Hon Kawu Sumaila ya
ce nan bada jima wa ba ne shugaban kasar zai
sake gabatar da cikakken bayani ga Majalisar.
Shirin rancen dai ya hada da sayar da takardun
bashi na kudin Euro da kuma shirin tallafawa
kasafin kudi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria: Ana cacar baki kan karbo rancen $30bn"

Post a Comment