Mun ji kunya da aka doke mu a gida - Pochettino

Kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya ce ba
wasan da suka yi a Wembley ba ne ya sa suka
sha kashi a hannun Bayer Leverkusen a gasar
cin kofin zakarun turai.
Bayer Leverkusen ta doke Tottenham da ci 1-0
ranar Laraba kuma hakan na nufin sun sha kashi
a dukkan wasannin cin kofin turai a gida a bana.
Pochettino ya ce: "Babu inda ba a samun
matsala a kwallon kafa a duk duniya. Matsalar a
wurinmu take ba a Wembley ba."
Tottenham na da zabi ta buga dukkan wasannin
lig na gida da kuma na cin kofin turai a Wembley
a kakar wasa mai zuwa.
Pochettino ya kara da cewa: "Wannan lamari
babban abin kunya ne a gare ni. Ba mu da wani
katabus ganin cewa mun yi wasa biyu a
Wembley, inda Monaco da Bayer Leverkusen,
suka kayar da mu. Laifin a wurinmu yake."

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Mun ji kunya da aka doke mu a gida - Pochettino"

Post a Comment