Nigeria: 'Ba son kai a yaki da cin hanci'

Gwamnatin Nigeria ta musanta zarge-zargen
cewa tana nuna son kai da siyasa a yaki da cin
hanci da rashawa.
Ministan shari'a na Najeriyar, Barrister Abubakar
Malami ya shaida wa BBC cewa duk wanda aka
samu da laifin wawure kudin gwamnati za'a
gurfanar da shi gaban kuliya.
Ya kara da cewa babu wata doka da gwamnatin
kasar ke karyawa wajen tsarewa da kuma
gurfanar da wadanda aka samu da laifin
almundahana da cin hanci da rashawa.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin
arzikin kasa ta`annati a Najeriyar dai na binciken
jami`ai da dama, kuma galibinsu na tsohuwar
gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan, lamarin
da ya sa wasu ke zargin cewa ana musu bi-ta-
da-kulli ne irin na siyasa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria: 'Ba son kai a yaki da cin hanci'"

Post a Comment