An taso keyar 'yan Ghana 108 daga Amurka

Gwamnatin Amurka ta taso keyar wasu 'yan
kasar Ghana su 108 zuwa kasarsu.
Mutanen dai sun hada da bakin-haure da
wadanda suka kawo karshen zaman su a gidan
kaso.
Wadansu daga cikinsu dai sun isa filin saukar
jiragen saman Accra, babban birnin kasar ta
Ghana, daure da ankwa da sarkoki.
Amurkar dai ta zarge su da kin ba da hadin kai
ga jami'an tsaro a lokacin da aka yi kokarin kama
su.
Gwamnatin Amurkar ta ce ta mayar da su Ghana
ne bisa zargin su da aikata laifuffuka daban-
daban, wadanda suka hada da safarar miyagun
kwayoyi, da sata da fyade da damfara, da kuma
fadace-fadace.
Mutanen dai sun musanta zarge-zargen, sun
kuma yi korafin cewa jami'an tsaron Amurka sun
muzguna masu.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An taso keyar 'yan Ghana 108 daga Amurka"

Post a Comment