Golan Leicester City ya tafi doguwar jiyya

Golan kungiyar Leicester Kasper Schmeichel zai
jima bai dawo filin wasa ba sakamakon raunin da
ya ji a hannunsa a karawar da suka yi da
kungiyar FC Copenhagen a gasar cin kofin
Zakarun Turai ranar Laraba.
Schmeichel, mai sheakara 29 ya ji raunin ne a
hannunsa na dama tun kafin a tafi hutun rabin
lokaci amma ya jure har aka tashi wasan
canjaras ba ci.
Kungiyar Leicester ta kafa tarihi a gasar ta
Zakarun Turai, na kasancewa wadda ta yi
wasanni hudu na farko ba tare da an ci ta ba.
Hukumar kungiyar ta Leicester ta ce dan wasan
dan kasar Denmark zai dauki tsawon lokaci kafin
ya dawo wasa.
Mai tsaron ragar ya kama wa kungiyar a
dukkanin wasanninta na gasar Premier 38 a
kakar da ta gabata da suka dauki kofi, inda ba a
zura masa kwallo a raga ba a wasanni 15.
Ya yi wa kulob din sama da wasanni 200 tun
lokacin da ya koma Leicester din daga Leeds
United a 2011, tun bayan da ya fara wasansa a
Manchester City.
Ron-Robert Zieler wanda dan tawagar kasar
Jamus ce da ta ci kofin duniya na 2014, mai
shekara 27 shi ne zai rika kama wa kungiyar
kafin Schmeichel ya warke.
Wasan da Zieler ya kama wa Leicester na karshe
shi ne wanda Manchester United ta ci su 4-1
ranar 24 ga watan Satumba.
Golan zai shiga raga ne a wasan Premier da
Leicester din za ta yi a gida da West Brom ranar
Lahadi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Golan Leicester City ya tafi doguwar jiyya"

Post a Comment