Ibrahimovic ya ci kwallo na 25,000 a tarihin Premier

Zlatan Ibrahimovic ya ci kwallo na 25,000 a
tarihin gasar Premier a ranar Lahadi, a wasan da
Manchester United ta doke Swansea City 3-1.
Paul Pogba ne ya fara ci wa United kwallo kuma
na 24,999, yayin da Ibrahimovic ya kara ta biyu a
minti na 21 kuma ta 25,000 da aka ci a gasar ta
Premier.
Haka kuma ta uku da Ibrahimovic ya ci wa
United ita ce ta 400 da ya zura a raga tun
lokacin da ya fara murza-leda a matsayin
kwararren dan kwallo.
Wannan ne karon farko da United ta ci kwallon
kirgen tarihi a gasar Premier, sai dai kuma ita ce
aka fara ci a gasar Premier da aka fara a
shekarar 1992.
Kuma Brian Deane ne ya zura wa United kwallo
da ka a raga, a lokacin da suka fafata da
Sheffield United a shekarar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ibrahimovic ya ci kwallo na 25,000 a tarihin Premier"

Post a Comment