An sake yin girgizar kasa a Italiya

Kasar Italiya ta sake fuskantar wata girgizar
kasar, kwanaki uku bayan wata girgizar kasa da
ba a taba ganin irinta ba cikin fiye da shekaru
talatin da biyar ta afkawa kasar.
Wani bincike da kwararru na Amurka suka
gudanar ya nuna cewa sabuwar girgizar kasar da
ta afkawa tsakiyar kasar, bata kai karfin wadda
ta faru ba a baya kuma kawo yanzu babu wani
rahoton barnar da ta yi.
Lamarin dai ya faru ne a kusa da kauyen Pieva
Taroni da ke kan tsaunin kudu maso gabashin
birnin Perugia.
Yawancin mazauna yankin dai sun yi gaggawar
barin kauyukan su tun bayan girgizar kasar da ta
faru tun a watan Agusta da ya wuce, da aka yi
asarar rayukan sama da mutane dari uku.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An sake yin girgizar kasa a Italiya"

Post a Comment