Sudan ta Kudu na fuskantar karuwar tarzoma-MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana fuskantar hadarin karuwar tarzoma da ka iya kai wa ga aikata kisan kare-dangi a Sudan ta Kudu.
Mashawarci na musamman ga Majalisar kan hana abkuwar kisan kare-dangi, Adama Dieng, shi ne ya bayyana haka a wani taron manema labaru a Juba.
Ya ce yakin basasar da ya barke a kasar kusan shekaru uku da suka gabata na ci gaba da ta'azzara tsakanin kabilu.
Mr Dieng wanda ya sha kai ziyara Sudan ta Kudu ya nuna damuwa kan irin abubuwa da yake gani a kasar inda ya bada misali da irin kashe-kashe da fyade masu nasaba da kabilanci, da kuma kona wasu kauyuka kurmus da aka yi a baya-bayan nan.
Babban jami'in ya kara da cewa yayin da shirin sulhu ya cije, mawuyacin halin da bil'adama ke ciki ke kara tsanani, kuma tattalin arziki ya tsaya cik, tare da yaduwar makamai a hannun jama'a, akwai alamomin tarzomar za ta ta'azzara.
Ya ce kisan kare-dangi al'amari ne da ya zama wajibi a kawo karshen sa, a don haka ya kamata a dauki mataki cikin gaggawa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Sudan ta Kudu na fuskantar karuwar tarzoma-MDD"

Post a Comment