Ambaliya ta kashe mutane a Afirka ta kudu


Ambaliyar ruwa ta mamaye birnin
Johannesburg da ke Afirka ta Kudu a wannan
makon bayan an shafe watanni ana fama da fari
Mutane da dama sun rasa rayukansu yayin da
wasu mutum 200 suka rasa muhallansu.
Wakilyar BBC, Nomsa Maseko ta ziyarci garin
Alexandra, inda nan ambaliyar ta fi kamari inda
wani mahaifi ya shaida mata cewa ambaliyar ta
tafi da 'yarsa.
Masu aikin ceto dai suna cigaba da neman
gawar yarinyar 'yar shekara uku.
Kungiyar bayar da agaji na taimakawa marasa
galihu da abinci sai dai ya zuwa yanzu babu
wata masaniya a kan inda za su kwana a daren
ranar Asabar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ambaliya ta kashe mutane a Afirka ta kudu"

Post a Comment