Uganda: Kotu ta yankewa jami'an gwamnati zaman kaso

An gurfanar da manyan jami'an gwamnatin Uganda uku gaban kuliya, da ake zargi da laifin yin al'mubazzaranci da kudaden fansho kusan dala miliyan ashirin da biyar.
Wata kotu a birnin Kampala ta samu bayanin jami'an sun bude sama da asusun ajiya a banki dubu biyu da sunayen bogi, daga bisani kuma suke rarraba kudaden a lalitar su.
An dai yanke musu shekara 10 kowanne a gidan kaso, amma su na da damar daukaka kara.
A bangare guda kuma za a yankewa wasu kananan ma'aikata biyar hukunci irin wannan duk dai kai batun.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Uganda: Kotu ta yankewa jami'an gwamnati zaman kaso"

Post a Comment