Shell ta rufe kamfanin Escravos a Najeriya

A Najeriya, kamfanin mai na Shell, ya ce ya
rufe tashar samar da iskar gas ta Escravos da ke
yankin Nija Delta mai azrikin man fetur.
Sanarwar na zuwa ne sakamakon zanga-zangar
da wasu mazauna yankin suka yi a ranar Laraba.
A cikin wani sakon email da ya aikewa manema
labarai, kamfanin na Shell din ya ce zai cigaba
da ayyukansa a Escravos din idan masu zanga-
zangar sun watse.
Masu zanga zangar sun kwashe kwanaki takwas
suna gudanarwa, inda suka yi korafin rashin
ababem more rayuwa a yankin.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Shell ta rufe kamfanin Escravos a Najeriya"

Post a Comment