Ya kamata a bai wa Southgate horar da Ingila - Rooney

Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Ingila,
Wayne Rooney, ya ce ya kamata a bai wa Gareth
Southgate aikin jan ragamar Ingila zuwa lokaci
mai tsawo.
Southgate ya jagoranci Ingila lashe wasanni biyu
daga guda uku da ya yi, inda a ranar Lahadi ya
samu nasarar doke Scotland a wasan shiga
gasar cin kofin duniya da ci 3-0.
Hakan ne ya sa Ingila ta dare mataki na daya a
kan teburin rukuni na shida, bayan da ta yi
wasanni hudu.
A kuma ranar Talata ne kociyan zai ja ragamar
Ingila a wasan sada zumunta da za ta yi da
Spaniya.
Southgate ya karbi aikin rikon kwarya na horar
da tawagar Ingila, bayan da hukumar kwallon
kafar kasar da Sam Allardyce suka raba gari.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ya kamata a bai wa Southgate horar da Ingila - Rooney"

Post a Comment