Tsohon dan kwallon Ivory Coast Laurent Pokou ya rasu

Tsohon dan wasan kwallon kafa na Ivory Coast
Laurent Pokou, wanda ake wa kallon wani kusa
a fagen kwallon kafa a nahiyar Afirka, ya rasu,
yana da shekara 69.
Laurent Pokou ya taka leda daga shekarun 1960
zuwa 1970 a kungiyar ASEC Mimosas inda ya
fara kwallonsa.
Ya buga wa kasarsa kwallo sau 70.
Pokou ya kuma buga kwallo a kulob din Nancy na
Faransa daga 1977 zuwa 1978, inda ya yi wasa
tare da Michel Platini.
Ana tuna shi saboda tarihin da ya kafa na zura
kwallaye mafiya yawa - 14 - da wani dan kwallo
tilo ya yi a gasar cin kofin kasashen Afirka.
Sai bayan shekara 30 sannan dan wasan Kamaru
Samuel Eto'o ya shafe wannan tarihi a shekara
ta 2008 a gasar da aka yi a Ghana.
Pokou ya mutu ne a birnin Abidjan bayan ya sha
fama da rashin lafiya.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Tsohon dan kwallon Ivory Coast Laurent Pokou ya rasu"

Post a Comment