Griezmann ba zai buga karawa da Real ba

Watakila dan wasan Atletico Madrid, Antoine
Griezmann, ba zai buga karawar da kungiyar za
ta yi da Real Madrid a ranar Asabar, sakamakon
raunin da ya yi.
Griezmann ya yi rauni ne a fafatawar da Faransa
ta ci Sweden 2-1 a wasan shiga gasar cin kofin
duniya da suka yi a ranar Juma'a.
Tuni dan kwallon ya koma Spaniya domin yin
magani, kuma hakan na nufin ba zai buga wasan
sada zumunta da Faransa za ta yi da Ivory Coast
ba a ranar Talata.
Atletico ce za ta karbi bakuncin Real Madrid a
wasan hamayya a gasar cin kofin La Liga
wasannin mako na 12 a ranar Asabar.
Griezmann mai shekara 25, shi ne dan wasan
Atletico da ya fi yawan ci wa kungiyar kwallaye a
kakar bana, inda ya ci guda shida.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Griezmann ba zai buga karawa da Real ba"

Post a Comment