Zan ci gaba da shirin inshorar lafiya na Obama- Trump

Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa zai ci gaba da tafiyar da shirin shugaba Obama na inshorar lafiya.
Soke shirin inshorar lafiyar da ake yiwa lakabi da Obama-care,na gaba-gaba cikin jerin abubuwan da Donald Trump ya yi ta nanata cewa zai yi a lokacin yakin neman zabe, yana mai cewa shirin tamkar wani babban bala'i ne ga kasar.
Su ma wasu shugabannin jam'iyyar Republican sun bayyana a babban taron jam'iyyar cewa tsarin inshorar lafiyar tamkar katsalandan gwamnati ke yi a harkar kiwon lafiya.
Sai dai yanzu a wata hira da ya yi da mujallar Wall Street Journal, zababben shugaban kasar ya nuna cewa zai iya ci gaba da aiwatar da wasu muhimman abubuwa dake kunshe a shirin inshorar lafiyar wadanda ya ce yana matukar so sosai.
Tun bayan nasarar da ya samu a zaben da aka yi ranar talata da ta wuce, Mista Trump ya ke ta sanar da sauye-sauyen da ya yi a lokacin yakin neman zaben sa.
Ya zuwa yanzu dai ya sauya fasalin mambobin kwamitin sa na karbar mulki inda ya ragewa gwamnan New Jersey Chris Christie mukami tare da nada zababben mataimakin shugaban kasa Mike Pence domin yasa ido akan nada jami'ai 4,000 kafin rantsar da shi a ranar 20 ga watan janairu.
Akwai kuma wasu mukamai da aka ware ga manyan 'ya'yan Mr Trump din su 3 da kuma wasu dake tsayawa kusa da shi a lokutan yakin neman zabe da suka hada da tsohon magajin garin New York Rudy Giuliani da tsohon kakakin Majalisar wakilai Newt Gingrich.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Zan ci gaba da shirin inshorar lafiya na Obama- Trump"

Post a Comment