WHO: Mutane fiye da 7,000 suka mutu a yakin basasa a Yemen

Wani bincike da kungiyar lafiya ra duniya WHO
ta gudanar ya gano cewa yakin basasa a kasar
Yemen ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da
dubu bakwai.
An kuma jikkata wasu mutane 37,000 a rikicin,
wanda aka soma a bara.
WHO tace fiye da rabin cibiyoyin lafiyar Yemen
din basa aiki yadda ya kamata ko kuma suna
rufe.
Kana likitoci sun ce mutane da dama na mutuwa
sakamakon ja'ibar yunwa.
Yakin ya jefa kasar cikin mawuyacin hali na
tabarbarewar tattalin arziki.
Yemen na daya daga cikin kasashe masu fama
da talauci a duniya.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "WHO: Mutane fiye da 7,000 suka mutu a yakin basasa a Yemen"

Post a Comment