Shugaba buhari yabada labarin abunda yafaru shekara 30 baya

– Shugaba Buhari ya bada labarin abin da ya
faru a shekarar 1985 bayan an hanbarar da
Gwamnatin sa
– An tsare Muhammadu Buhari na watanni da
dama a Birnin Benin bayan an yi masa juyin
mulki
– Marubucin tarihin Shugaba Buhari ya bayyana
yadda abin ya faru
Shugaba Buhari ya je Garin Benin na Jihar Edo
wani ziyara na kwana biyu domin kaddamar da
ayyukan Gwamna mai barin gado-Adams
Oshiomole. Shugaba Buhari ya bayyana yadda
aka tsare sa a Garin Benin shekaru fiye da
talatin da suka wuce bayan an kifar da
Gwamnatin sa.
Bayan kaddamar da ayyukan Gwamna
Oshiomole, Shugaba Buhari ya tunawa Jama’a
cewa ya zauna a wannan gari na wata da
watanni . Buhari yace: Nayi matukar farin cikin
zuwa bude wadannan ayyuka na Gwamna
Oshiomole. Mutane da dama ba su san na zauna
a wannan Gari ba har na watanni 40 a wani dan
karamin gida, bayan an yi mani juyin mulki a
shekarar 1985.
Mawallafin Littafin Tarihin Shugaba Buhari,
Farfesa Paden a cikin Babin da yayi magana
game da Kalubalen Shugabanci a shafi na 33 na
Littafin yayi bayanin yadda aka tsare Shugaba
Buhari a Garin na Benin bayan an hanbarar da
Gwamnatin sa.
A lokacin nan, an tsare Muhammadu Buhari ne a
wani dan gida, aka hada shi da wani dan
Talabijin domin sauraron labarai, sannan ana
kawo masa jaridu, da abinci a kan kari. Buhari
ya rika karanta Al-Qurani da littatafai.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Shugaba buhari yabada labarin abunda yafaru shekara 30 baya"

Post a Comment