An garzaya da Maryam Ali zuwa Maiduguri

Wata majiya daga babban ofishin rundunar
mayakan sojan sama ta bayyana cewa sun
garzaya da daya daga cikin yan matan
Chibok da aka kwato Maryam Ali Maiyanga
zuwa garin Maiduguri a jirgi mai tashin
angulu a ranar Litinin, 7 ga watan Nuwamba.
Idan za’a iya tunawa, da misalin karfe 6 na
safiyar asabar 5 ga watan Nuwamba ne aka
gano Maryam Ali yayin da Sojoji ke tantance
mutanen da suka tsere daga dajin Sambisa a
garin Polka, karamar hukumar Gwoza, inda
daga nan ne aka garzaya da ita tare da
yaron ta mai watanni 10 data same shit a
hanyar aure da wani kwamandan kungiyar.
A ranar 14-15 na watan Afrilun shekara ta
2014 kungiyar Boko Harama ta sace yan
mata 276 daga makarantar Chibok dake jihar
Borno. Rahotanni sun bayyana cewa an aurar
da Maryam ga wani kwamandan Boko
Haram.
Sai dai tun a baya an samu yan mata 57 da
suka tsere daga hannun kungiyar, inda kuma
kungiyar ta sako wasu 21 bayan wata
yarjejeniya tsakaninsu da gwamnati. A yanzu
haka jama’a na sa ran sauran matan ma
zasu fito.
A watan Mayun 2016 ne aka gano daya daga
cikin yan matan mai suna Amina, tace
sauran matan na nan a hannun Boko Haram,
amma fa 6 daga cikinsu sun rasu. Bayan sati
daya ne aka sake gano daya daga cikin su,
sai dai iyayen yan matan sun musanta cewa
taa cikinsu, saboda babu sunan ta a jerin
sunayen wadanda aka sace. Sai a watan
Oktoban bana aka sako yan mata 21.
Wadannan sune kalubalen da gwamnati ke
fuskanta, ana sa ran gwamnati na
tattaunawa da yayan kungiyar don sako
sauran yan mata 83 da suka rage a hannu.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An garzaya da Maryam Ali zuwa Maiduguri"

Post a Comment