Yan bindiga sunyi garkuwa da mutane 5 a jihar Ekiti

– Anyi garkuwa da mutane 5 a jihar Ekiti
– Wannan ya faru ne a ranan Asabar, 5 ga
watan Nuwamba
– Kakakin jam’ian yan sandan jihar ya
tabbatar da hakan
Anyi garkuwa da mutane 5 a jihar Ekiti, jihar
mai maganan nan Ayo Fayose a ranan
asabar, 5 ga watan Nuwamba 2016.
Game da cewar NAN, wadanda akayi
garkuwa da su sune Fasto Ojo da direbansa
da kuma wasu guda 3.
Sun kasance suna bulaguro ne zuwa karamar
hukumar Ise/Orun na jihar inda hakan ya
faru. Kakakin jami’an yan sandan jihar,
wanda ya tabbatar da faruwan yace an saki
mutane 2 daga cikinsu.
Yace jami’an yan sanda na kan hanyan ceto
sauran guda 3 da akayi garkuwa da du. Yayi
kira da mutanen unguwan su taimaka way an
sanda wajen sanun makafan su.
Wannan na faruwa ne kwanan da ya kacal
bayan akayi garkuwa da sakataren hukumar
gudanar d zaben jihar EKiti, Barrista Muslim
Olujide Omoleke.
Anyi garkuwa da Barrister Muslim Olujide
Omoleke ne da yaronsa da kuma direba a
titin Ilesha/Akure a ranan juma’a.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Yan bindiga sunyi garkuwa da mutane 5 a jihar Ekiti"

Post a Comment