Wanene Laftanar Kanar Muh'd Abu-Ali?

Labarin rasuwar kwamandan rundunar sojin
Najeriya ta 272 mai kula da tankokin yaki,
Laftanar Kanar Muhammad Abu-Ali, shi ne
kusan batun da yafi kowanne jan hankalin
ma'abota shafukan sada zumunta a Najeriya a
ranakun karshen mako.
Laftanar Kanar Abu-Ali yana cikin sojoji biyar da
suka rasa rayukansu a daren Juma'a, yayin bata
kashi da mayakan kungiyar Boko Haram da suka
kai hari kan wani barikin soji dake Mallam Fatori
a jihar Borno, dake arewa maso gabashin
Najeriya.
Rundunar sojin Najeriyar ta sha bayyana
dakarunta da su ke rasa rayukansu a rikicin Boko
Haram, a matsayin jarumai, wadanda suka
sadaukar da rayukansu don kare rayukan sauran
jama'ar kasar.
Sai dai a wurin hukumomin sojin Najeriyar,
jaruntar Laftanar Kanar Muhammad Abu-Ali ta
daban ce. Hakan ne ma yasa ya samu karin
girma na daban a cikin yakin da ake yi da Boko
Haram.
A watan Satumban 2015 a Gamboru Ngala,
babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar
Janar Tukur Buratai ya yi mushi karin girma daga
Manjo zuwa Laftanar Kanar tun kafin ya kai
shekarun samun karin girman.
Wace irin jarumta ya nuna?
A cikin sanarwar sojin kasar wacce ta tabbatar
da kashe Laftanar Kanar Abu-Ali, kakakin
rundunar sojin kasa ta Najeriya, Kanar Sani
Usman Kukasheka ya bayyana shi a matsayin
sojan da ya nuna jarunta ta daban.
Hakanne a cewar shi, ya sa aka yi mushi karin
girma tun kafin ya cika shekarun samun karin
girman.
A wata hira da Bilkisu Babangida, Kanar
Kukasheka ya ce idan ana neman jarumin soja,
to in aka samu Laftanar Kanar Abu-Ali, babu
sauran magana kuma:
Masu sharhi da marubuta da dama a Najeriyar
sun ce mariganyi Laftanar Kanar Abu-Ali, ya yi
suna ne a yakin da dakarun kasar ke ci gaba da
yi na kawar da kungiyar Boko Haram.
A wani rubutu na girmamawa ga mamacin,
Hamza Idris, tsohon ma'aikacin jaridar Daily
Trust a arewa maso gabashin Najeriya, ya
bayyana shi a matsayin mutun mai zuciya irin ta
zaki, sarkin daji wanda ba ya gudu, ba ya ja da
baya har zuwa lokacin da rayuwarshi ta kare.
A cewar Idris, mutanen jihar Borno, wadanda su
ne suka fi shan wahalar rikicin Boko Haram, su
ne za su fi kowa sanin wanene Laftanar Kanar
Abu-Ali, saboda a cewarshi, Laftanar Kanar Abu-
Ali, ya na gaba-gaba a cikin sojojin da suka
sarrafa manyan makaman da aka girke a arewa
maso gabashin Najeriya domin yaki da Boko
Haram.
Tun a watan Yunin wannan shekara, lokacin da
ba wanda ya kawo cewa ta Allah za ta faru da
Laftanar Kanar Abu-Ali a wannan lokaci, Editan
jaridar TheCable, wacce ake wallafa wa a
intanet, Fisayo Soyombo ya yi rubutu na
jinjinawa jarumtar sojan.
Soyombo ya ce kamar yadda rahotanni suka
nuna, jaruntar da Laftanar Kanar Abu-Ali ya nuna
wajen sarrafa tankokin yaki, ita ta taimaka sojoji
suka kwato garin Baga da Gamboru-Ngala daga
hannun kungiyar Boko Haram.
Wasu sojoji da suka yi aiki a karkashinsa, sun
shaida wa BBC cewa samun jagora irin Laftanar
Kanar Abu-Ali ya na da wuya, domin shi mutun
ne mai karfafa gwiwar na kasa da shi, da kula da
bukatunsu, da shiga gaba a duk inda aka dosa.
Marigayin dan asalin jihar Kogi a tsakiyar
Najeriya ne, kuma da ne ga basaraken
masaraunar Nge, Birgediya Janar Abu Ali mai
ritaya.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Wanene Laftanar Kanar Muh'd Abu-Ali?"

Post a Comment