An gano kokunan kan mutane 40 a Bangladesh

'Yan sanda a Bangladesh sun gano kokunan kan
mutun guda 40, da wasu kasusuwan mutane a
wani gida a Dhaka, babban birnin kasar.
'Yan sandan sun kuma kama wani dalibi dake
karatun aikin likita.
Wani jami'in 'yan sandan ya shaidawa BBC cewa
dalibin da aka kama, ya amsa cewa yana sayar
da kasusuwan mutanen ne ga daliban dake
karatun aikin likita akan kudi dala 450 kowanne
daya.
Ana gani dalibin yana tono kasusuwan mutanen
ne a makabartu a wajen birnin, sannan ya wanke
su da sinadarai da sauran kayan aiki.
'Yan sandan yanzu, suna na kokarin gano sauran
mutanen da yake sana'ar tare da su.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An gano kokunan kan mutane 40 a Bangladesh"

Post a Comment