'Yan Boko Haram 240 sun mika wuya bayan farmakin soji

Mayakan Boko Haram fiye da 240 ne suka mika
wuya, bayan farmaki ta sama da kasa da
dakarun hadin guiwa na kasa da kasa (MNJTF)
suka kai a maboyarsu.
Wata sanarwa da rundunar ta MNJTF ta fitar, ta
bayyana cewa yawancin mayakan sun fito ne
daga yankin na tafkin Chadi.
Ta kara da cewa mayakan sun mika wuyan ne a
sashe na biyu na sansanin soja a yankin
Bagasola da ke kasar Chadi.
Dakarun na MNJTF da suka fito daga Najeriya,
Chadi, Nijar da Kamaru sun fara aikin murkushe
mayakan Boko Haram din da ke kasashen da aka
yiwa lakabi da ''Operation Gama Aiki''.
An kuma tantance su tare da ajiye su a sansanin,
inda Kwamandan rundunar Manjo Janar Lamidi
Adeosun ya yi musu jawabi.
Kwamandan ya ce za a ba su horo a fannoni
daban-daban na sana'oi, kamar yadda hukumomi
da wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka
tsara.
Sojojin dai sun samu galabar toshe kafofin
samun abinci da kayan fada zuwa ga mayakan,
da hakan ya sa su da iyalansu kaura daga
matsugunansu suka mika wuya.
Galibinsu dai sun mika makamansu a sansanonin
soji mafi kusa da su a yankin.
Hakan dai ya kawo adadin mayakan na Boko
Haram da suka mika wuyansu zuwa 460 kawo
yanzu.
Bayanai sun nuna cewa akwai mayakan Boko
Haram da dama a yankin na tafkin Chadi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "'Yan Boko Haram 240 sun mika wuya bayan farmakin soji"

Post a Comment