'Yan Nigeria na goyon bayan Clinton a zaben shugaban Amurka

'Yan Nigeria da dama na goyon bayan Hillary
clinton, 'yar takarar shugabancin Amurka a
karkashin jam'iyyar Democrat domin zamo wa
shugabar kasa.
Mutane da dama a kasar sun damu cewa akwai
yiwuwar hana shiga kasar, idan har Donald
Trump abokin hamayyarta ya ci zaben.
Tuni dai Wole Soyinka, shahararren marubucin
nan ya ce zai yaga takardarsa ta Green Card,
wadda ke ba shi damar zama a Amurka kuma ya
bar kasar idan har Mista Trump ya yi nasara.
Har ila yau dai 'yan Najeriyan na tsoron makomar
'yan uwansu da ke zaune a Amurka, da kuma irin
tasirin da zai yi a kan rayuwarsu idan Donald
Trump ya lashe zaben.
Najeriya dai na cigaba da fuskantar matsin
tattalin arziki da tsada rayuwa.
Mutane da dama na dogaro ne da 'yan uwansu
da ke kasashen waje domin su tallafa musu.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "'Yan Nigeria na goyon bayan Clinton a zaben shugaban Amurka"

Post a Comment