Niger: 'Yan bindiga sun kashe sojoji biyar a Nijar

Akalla sojoji biyar ne aka kashe, a yayin da
wasu hudu kuma suka bace bayan wani hari da
aka kai garin Banibangu da ke jihar Tilabery a
Jamhuriyar Nijar.
Rahotanni da aka ysamu daga yankin Banibangu
da ke jihar Tilabery wanda ke iyaka da kasar
Mali, wasu 'yan bindiga suka kai wa garin hari.
Ya zuwa yanzu dai ba a tantance ko su wanene
ba, suka kai harin, amma ana zargin mayakan
sun fito ne daga Malin.
Za ku iya sauraron karin bayani a rahoton da
wakilinmu Baro Arzika ya aiko mana a farkon
wannan shafi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Niger: 'Yan bindiga sun kashe sojoji biyar a Nijar"

Post a Comment