Za a kaddamar da yakin kwato Raqqa

Wasu mayakan Kurdawa da Larabawa, wadanda
Amurka ke goya wa baya sun ce za su kaddamar
da yakin kwato Raqqa, inda aka ce shi ne
babban birnin da ke hannun kungiyar IS a Syria.
Mayakan kungiyar Syria Democratic Forces
(SDF) sun ce gamayyar rundunar da Amurka ke
jagoranta ce za ta taimaka musu da kai hare-
hare ta sama nan da sa'oi kadan masu zuwa.
Sun gargadi farar hula da ke birnin da su fice
daga unguwannin da mayakan IS suke.
Mayakan na Kurdawa da Larabawa dai sun
mamaye unguwanni da dama na arewacin birnin.
Za su kaddamar da hare-haren ne a daidai
lokacin da dakarun Iraqi wadanda Amurkawa ke
goyon baya ke ci gaba da kokarin korar mayakan
IS daga birnin Mosul inda suka fi karfi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Za a kaddamar da yakin kwato Raqqa"

Post a Comment