An kashe 'yan kunar-bakin-wake a Maiduguri

Rahotanni daga birnin Maiduguri na jihar Borno
da ke Najeriya na cewa an kashe wasu 'yan
kunar-bakin-wake da suka yi yunkuri tayar da
bama-bamai da safiyar Juma'a.
Jamai'an tsaro sun shaida wa BBC cewa
maharan uku, wadanda dukkan su mata ne, sun
yi yunkurin shiga birnin Maiduguri ne amma an ci
lagonsu aunguwar Ummurari da ke wajen birnin.
Kungiyar Boko Haram ce dai ke kai hare-hare a
birnin da ma wasu yankuna na jihar ta Borno da
makwabtan jihohi.
Sai dai rundunar sojin Najeriya ta ce tana ci gaba
da fatattakar mayakan kungiyar, kuma nan ba da
dadewa ba za ta kawar da ita daga doron kasa.
Ko a makon jiya sai da mayakan kungiyar suka
kashe wasu sojin Najeriya, cikin su har da
Latftanar Kanar Muhammad Abu Ali, wani soja
da ya yi suna wajen ragargazar mayakan Boko
Haram.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An kashe 'yan kunar-bakin-wake a Maiduguri"

Post a Comment