An yi asarar $600bn saboda boren da aka yi a kasashen Larabawa

Juyin-juya-halin da aka yi a kasashen Larabawa
ya sanya yankin ya yi asarar kusan $614, in ji
wata hukuma ta majalisar dinkin duniya.
Wannan kiyasi shi ne na farko da aka yi kan
tasirin da boren ya yi a fannin tattalin arzikin
yankin.
Hukumar da ke nazari kan tattalin arziki da
walwala a yankin yammacin Asia ta ce asarar ta
yi daidai da kashi shida na kudaden da kasashen
Larabawa za su samu daga shekarar 2011 zuwa
2015.
Boren, wanda aka soma daga kasar Tunisia, ya ci
rawanin shugabanni kasashe hudu, kuma ya
haddasa rikici a kasashen Libya, Syria da kuma
Yemen.
Hukumar ta yi kididdiga kan irin kudaden da take
ganin yankin zai samu da a ce ba a yi juyin-juya-
halin ba kafin ta fitar da wadannan bayanai.
Ta sanya kasashen da rikicin bai shafa kai-tsaye
ba a cikin rahotonta, saboda irin tasirin da
faruwar rikicin ya yi a kan su.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An yi asarar $600bn saboda boren da aka yi a kasashen Larabawa"

Post a Comment